56وَكَذٰلِكَ مَكَّنّا لِيوسُفَ فِي الأَرضِ يَتَبَوَّأُ مِنها حَيثُ يَشاءُ ۚ نُصيبُ بِرَحمَتِنا مَن نَشاءُ ۖ وَلا نُضيعُ أَجرَ المُحسِنينَAbubakar GumiKuma kamar wancan ne Muka bãyar da ĩko ga Yũsufu a cikin ƙasa yanã sauka a inda duk yake so. Munã sãmun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma bã Mu tõzartar da lãdar mãsu kyautatawa.